Gwamnatin Tarayya ta fara shirin cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa da wasu sassa da ke karkashin fadar gwamnatin ga ’yan kasuwa.
Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar, ya ce Ma’aikatar Kudi da Kasa tare da Fadar Shugaban Kasar sun ware wasu ayyuka da tsare-tsare uku a Fadar Shugaban Kasa da gwamnati za ta fara yin hadaka da ’yan kasuwa wajen gudanar da su.
- Wutar Lantarki: Minista ya ba da umarnin dawo da wutar Kano
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara
Ya bayyana cewa Asibitin Fadar Shguaban Kasa da ke Abuja da Legas daya ne daga bangarorin da ake shirin shigo da ’yan kasuwa su zuba jari.
Sauran su ne Sashen Kula da Gandun Daji da kuma Dandalin Wasan Yara na Fadar Shugaban kasa.
Tijjani Umar ya sanar da haka ne a jawabinsa ga taron wata uku na farkon shekarar 2023 kan hadakar gwamnati da kamfanoni da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa.
A watannin baya Shugaba Buhari ya sanya aikin gina sabbin bangarori na bayar da kulawa na musamman a asibitin a kasafin 2023.
A baya yanayin da Asibitin Fadar Shugaban Kasa ke ciki ya tayar da kura, musamman bayan da matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi korafi game da rashin magunguna da kayan aiki a asibitin.
’Yan Najeriya na yawan yin ce-ce-ku-ce game da yadda Shugaba Buhari ke zuwa duba lafiyarsa a kasashen waje.
A watannin baya dai Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin yin dokar hana jami’an gwamnati zuwa duba lafiyarsu a kasashen waje, da nufin inganta yanayin bangaren lafiyar Najeriya.
Bangaren lafiyan Najeriya na fama da karancin likitoci, inda kwararrun likitoci ke tururuwar barin kasar domin yin aiki a kasashen waje.
Kungiyar likitoci ta Najeriya (NMA) ta bayyana cewa kasa da likitoci 15,000 ne suka rage a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan 200.
A kan haka ne majalisar dokoki ta kasa take kokarin yin dokar da zai wajabta wa wadanda suka kammala karatu a fannin likita yin aiki aiki na shekara biyar a kasar kafin a ba su lasisi.