Gwamnatin Tarayya ta amince ta bai wa malaman jami’o’i Naira Biliyan 30 a matsayin alawus dinsu na karatu (Earned Academic Allowance).
Gwamnatin ta ce za ta fara biyan su kudin ne da kadan-kadan daga watan Mayu, 2021 har zuwa Fabrairu, 2022.
- IPPIS: Gwamnati da malaman jami’a za su hau kan teburi
- Kungiyar Izala ta aza harsashin gina jami’a
- Yadda malaman jami’a suka yi sabani da ASUU
Hakan na daga cikin yarjejeniyoyin da suka cimmawa a tattaunawar gwamnatin da Kungiyar ASUU ta malaman jami’o’in, a ranar Alhamis.
Domin farfado da bangaren ilimi, gwamnati ta yi alkawarin kashe Naira biliyan 20, a matsayin domin kawo karshen yajin aiki watanni bakwai da ASUU ta shiga.
Kafin su shiga taron, Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya ce an yaudari dalibai ne suka shiga cikin zanga-zangar #EndSARS kasancewar jami’o’i a kulle su ke, kuma ASUU na yajin aiki.
Ya kuma yi fatar ’yan ASUU za su koma aiki kwanan nan saboda gwamnati na bin hanyoyin da kawo karshen yajin aikin.
Ngige ya ce, “Mun kwashe fiye da mako daya muna kai-kawo; muna tattaunawa kuma da yardar Allah hakar za ta cimma ruwa”.
Jami’an gwamnati da Ngige ya jagoranta a zaman sun hada Minista a Ma’aiatar Kwadago, Festus Keyamo (SAN), da sauran masu ruwa da tsaki; shi kuma Shugaban Kungiyar ASUU, Farfessa Biodun Ogunyemi, ya jagoranci mutanensa.