Gwamnatin Jihar Osun ta gargadi jama’a kan su guji shan ruwan rafin Osun saboda gurbacewa.
Gwamnatin ta yi wannan gargadi ne duba da yadda jama’a daga ciki da wajen jihar za su hadu wajen bikin gargajiya na shekara-shekara da zai gudana a ranar Juma’a.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kwadayi Ya Kai ’Yan Najeriya Tashar Wulakanci A Aljeriya
- Mun kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Rafiu Isamotu ne ya yi wannan gargadi a madadin gwamnatin jihar yayin wata tattaunar da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Osogbo ran Alhamis.
Isamotu ya ce gwamnati a dauki matakin fadakar da mutane game da shan ruwan rafin ne bayan da ta gano aikin masu hakar ma’adinai a yankin ya gurbata ruwan wanda ka iya yi wa mutum illa idan aka sha.
Ya kara da cewa, za a girke jami’an kiwon lafiya a wajen bikin don ci gaba da wayar da kan jama’a kan illar da ke tattare da shan ruwan.
(NAN)