Gwamnatin Tarayya ta umarci makarantu a dukkannin matakai su fara shirin budewa a fadin Najeriya.
Shugaban Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa, Dakta Sani Aliyu a bayyana haka a jawabin kwamitin na ranar Alhamis.
“Makarantun raino da firamare da sakandare da manyan makarantu da cibiyoyin ilimi su fara shirye-shiryen budewa a matakin.
Sai dai ya ce, “Muna shawartar da a yi cikakken bincike domin tantance yayanin hadari domin tabbatr da cewa dukkanin mataku sun tanadi dukkanin kaya da matakan kariya da kuma tabbatar da bin dokokin”.
A watan Maris aka rufe makarantu a Najeriya bayan bullar cutar COVID-19 kafin a sake budewa a ranar 4 ga Agusta ga dalibai masu rubuta jarabawar kammala firamare da kuma karama da babbar sakandare.
“Wuraren raino makarantu za su kasance a rufe har sai an gama tantance yanayi hadarin.
“Idan aka tashi bude makarantun, dole ne ya zama mataki-mataki domin kawar da barazanar ga al’umma da mutane masu rauni da ke iya kamu da cutar”, inji Dakta Sani.
NYSC ta fara shirin bude sansanoninta
Ya kuma bukaci Hukumar Kula da Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta fara shirin bude sansanoninta da zarar makarantu sun bude.
Ya ce gwamnati ke shirin samar NYSC da isassun kayan kariya gabanin bude sansanonin.
“Muna kokarin fitar da tsauraran matakan tabbatar da ba a samu bullar cutar COVID-19 ba idan aka fara” inji shi.