✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta umarci ma’aikata daga mataki na 12 su dawo aiki

Gwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikatanta da ke kan matakai na 12 da 13 da wadanda suke ayyukan da suka zamo dole su fara zuwa aiki…

Gwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikatanta da ke kan matakai na 12 da 13 da wadanda suke ayyukan da suka zamo dole su fara zuwa aiki kullum.

Shugabar Ma’aikata ta Kasa, (HoSCF), Folashade Yemi-Esan, ta bayar da umarnin a ranar Litinin, 10 ga watan Augusta, 2020.

Ta ce wadanda suka dawo aiki za su rika zuwa daga karfe 8:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, a ranakun Litinin zuwa Juma’a.

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar kwamitin shugaban kasa na yakar COVID-19 cewa ma’aikatan da ke tsallake ranaku zuwa aiki su fara zuwa kullum.

Gabanin sanarwar, ma’aikatan da ke mataki na 14 zuwa sama ne kadai ke zuwa aiki sau uku a mako domin kauce wa yaduwar COVID-19.

Ta kuma umarci manyan sakatarori da shugabannin ma’aikatun gwamnati su maido ma’aikatan da ke gudanar ayyukan tilas bakin aiki.

“A kula da abubuwan da ka iya jawo matsalolin lafiya in har mutane suka dawo, daidai da ka’idojin da aka gindaya na COVID-19″.

Ta kuma yi kira ga ma’aikatan da su bi ka’idojin na hana kamuwa da cutar da suka hada da bayar da tazara da wanke hannu da sanya amawali.

“Inda kuma aka dawo da yawa, to shugabanin ma’aikatan su raba ma’aikatan a rika yin tsarin karba-karba”.