Sanata Ali Ndume (APC, Borno ta kudu) ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bar bata lokacinta wajen saita tunanin ‘yan Boko Haram saboda a cewarsa ba za su taba tuba ba.
Ndume, ya ce da yawa daga cikin wadanda gwamnati ta saita tunaninsu ta kuma maido su cikin al’umma sun koma kashe-kashensu.
A hirar da BBC Hausa ta yi da shi, dan Majalisar Dattawan ya ce, “Mafi yawa daga cikinsu da suka fito sun koma. Ba za su taba gyaruwa ba. Gwamnati ta san yadda za ta yi da su.
“Wadannan mutane ne kamar khawarijawa (baudaddu). Gwamnati ta san yadda za ta yi da su amma ba dai a kawo wa mutum wanda ya kashe mar mahaifi ko dan’uwa ba.
“Kuma ba wai ya tubar maka ba ne, gwamnati ya tubar mawa. Yana ganin kamar gwamnati ce ta kasa shi yasa ta lallabe shi ya dawo cikinsu”.
Ndume ya ce jama’arsu ba su gamsu da shirin na gwamnati ba don haka “ya kamata a dakatar da shi”.
“Idan da gaske ake yin wannan abun to wadanda suke sansanin gudun hijira ya kamata a koya wa sana’o’i don su taimaki rayuwarsu”, inji Ndume.
A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya ta yaye tsofaffin ‘yan Boko haram 600 a shirin nata da sojin kasa suka kirkira a karashi shirin Operation Safe Corridor, a shekarar 2016.
Makasudin kirkirarar sa shi ne saita tunanin ‘yan Boko haram din da kuma sake mayar sa su cikin al’umma.
Shirin dai ya fuskanci kalubale musamman daga mutanen da ‘yan kungiyar suka kashe musu iyaye da yan’uwa ko mata da aka kashe musu mazaje aka bar su da marayu.