Gwamnatin Jihar Gombe ta rushe wani gidan gala da ake kokarin sake ginawa a unguwar Mil Uku da ke birnin Gombe, duk da umarnin dakatarwar da ta bayar a baya.
A kwanakin baya ne gwamnatin ta sanar da rufe gidajen gala, a fadin jihar inda daga bisani ta sa duk a rushe su.
Sai dai bayan aiwatar da rushe-rushen, an samu wasu da ta kira masu kunnen kashi da suka sake yunkurin gina gidan da aka rushe kafin daga bisani Hukumar Tsara Birane ta jihar (GOSUPDA) ta sake rusa shi.
A cewar gwamnatin rushe gidajen wani tsari ne na inganta tarbiyya da hana aikata miyagun laifuffuka ta hanyar haramta ayyukan gidajen rawar .
Da yake zantawa da manema labarai a Gombe ranar Asabar, Babban Daraktan hukumar, Bappayo Samanja Maudo, ya ce ya yi tattaki ne don ganewa idonsa yadda aikin rusau din ya gudana.
Bappayo Samanja, ya kuma ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da bin wannar doka sau da kafa.
Daga nan sai ya gargadi masu irin wannan hali su shiga taitayinsu, domin GOSUPDA a shirye take ta sanya kafar wando daya da duk masu kunnen kashi da suka bijire wa umarnin.