✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta rufe kwalejojin ilimi 39 a Bauchi

Ba su samu amincewar Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Kasa (NCCE) ba.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta rufe kwalejojin ilimi masu zaman kansu guda 39 saboda rashin rijista.

Kwamishinar Ilimi ta jihar, Madam Lydia Tsammani ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Bauchi a ranar Alhamis.

Tsammani ta ce cibiyoyin da lamarin ya shafa ba su samu amincewar Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Kasa (NCCE) ba, ko kuma ta samar da ababen gudanar da harkokin kwalejojin.

“An gano jimillar kwalejoji 39 ba su da komai. Suna gudanar da ayyukansu a wasu makarantun firamare.

“Da zarar an tashi daga makarantun firamaren sai a fara shirin karatun NCE har da malaman firamare da sakandare a matsayin malamansu.

“Sukan ma yi aron malamai saboda ba su da abin da zai sa su tsaya a matsayin kwalejin ilimi mai zaman kanta,” in ji ta.

A cewar Tsammani, ma’aikatar ta bayar da sanarwa ga kwalejojin da ba su yi rajista ba tare da tsare-tsaren da aka amince da su.

Ta kume ce an bukaci da su kammala rajistar su cikin watanni shida ko kuma su fuskanci tara.

Ta ce, za a bar kwalejoji 12 da suka samu amincewar NCCE su ci gaba da aiki ne kawai bayan sun samar da ƙwararrun ma’aikata tare da biyan kuɗaɗen rajista ga ma’aikatar.

“Dole ne su tabbatar sun ɗauki ɗalibai da suka cancanta ne kawai domin an gano cewa wasu daga cikinsu suna son biyan kuɗin makaranta ne kawai.