✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Gwamnati ta kwato Naira biliyan 11 sakamakon bayanan-fallasa da ta samu”

Ministan Kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun ta ce Gwamnatin Tarayya ta gano tare da kwato Naira biliyan 11 da digo shida sakamakon bayanan-fallasa da ta…

Ministan Kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun ta ce Gwamnatin Tarayya ta gano tare da kwato Naira biliyan 11 da digo shida sakamakon bayanan-fallasa da ta samu tun da aka kaddamar da dokar bayanan-fallasa a watan Disamban 2016.
Da take jawabi jiya a Abuja a taron karawa juna sani karo na biyar kan sake garambawul ga aikin gwamnati wanda aka yi wa lakabi da “Dokar Fallasa Amfaninta ga Ma’aikatan Gwamnati”, Adeosun ta ce daga cikin bayanan-fallasa dubu biyar da gwamnati ta samu, gwamnati ta bi diddigin bayanai 365 kuma ta biya mutum 20 da suka kwarmata bayanan naira miliyan 375 da digo takwas.
Ta bayyana cewa dokar fallasa ta zama daya daga cikin sabbin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su.
Ta kara da cewa gwamnati ta samu fiye da rabin bayanan-fallasar daga ma’aikatan gwamnati kan batutuwan da suka shafi kara kudin kwangila da ma’aikatan bogi da daukar ma’aikata ba bisa ka’ida  ba da barnar kudi da sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba da karkatar da kudin shigar gwamnati da kuma karya ka’idar dokokin yin amfani da asusun baidaya da makamantansu.