✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti domin samo hanyoyin magance rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.Kwamitin yana karkashin…

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti domin samo hanyoyin magance rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.
Kwamitin yana karkashin shugabancin Babban-Daraktan Makarantar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya da Sasanci (IPCR), Farfesa Oshita O. Oshita ne.
Wata takarda da Mukaddashin Babban-Sakatare a Ma’aikatar Cikin Gida, Alhaji Muhammadu Maccido ya sanya wa hannu, ta ce kwamitin zai fito da tsare-tsare da hanyoyin da za a shawo kan lamarin rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda za a tsara wani babban taro na masu ruwa-da-tsaki domin samar da mafita.
Takardar ta ce a yayin taron, akwai yiwuwar a fitar da tsari da hikimomin da masu ruwa-da-tsaki za su samar ta hanyar tattaunawa, kan yadda za a magance rashin jituwa a tsakanin manoma da makiyaya. Za a tattauna domin gano matsalolin da suke haifar da al’amarin da kuma maganinsu. Haka kuma tattaunawar za ta duba yadda al’amarin yake a nahiyoyi da kasashen duniya, tare da duba dokokin kasashen duniya da suka danganci al’amarin.
A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin, Oshita ya ce samar da wannan kwamiti ya nuna kyakkyawar niyyar wannan gwamnati, wajen samar da zaman lafiya da lumana a tsakanin al’ummar kasar nan. Ya ce, ya kamata kowane dan kasa ya ba da gudunmawar da ta kamata, sannan ya ba da goyon baya ga gwamnati domin bunkasa kasar nan.