Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci gaban Al’umma (CITAD) ta yaba wa Gwamnatin Tarayya game da kiran da ta yi ga al’ummar kasar nan su guje wa yin amfani da kalman batanci don gudun haifar da tashin hankali a kasar nan.
Babban Jami’in Shirye-Shirye na Cibiyar CITAD Malam Isah Garba ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a wajen taron da cibiyar ta saba shiryawa duk wata a Kano.
Malam Isah Garba ya ce sakamakon kiraye-kirayen da cibiyarsu ke yi da wadansu mutane game da illar amfani da kalaman batanci ya sanya an samu ci gaba wajen wayar da kan jama’a a wannan fanni, musamman kalaman da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yi kan hakan a wurin taron hadin kan kasa. “Abin sha’awa sai ga shi Mukaddashin Shugaban Kasa ya bayyana illar da kalaman batanci ke jawowa inda aka ruwaito shi yana cewa: “Tarihi ya nuna cewa yawancin riginginmun da ake samu a tsakanin al’umma kalaman batanci ne ke haddasa su, inda ya ce ana amfani da kafafen watsa labarai musamman kafafen sada zumunta na Intanet wajen watsa irin wadannAn kalamai na batanci,” inji shi.
Sai dai Cibiyar CITAD ta yi kira ga gwamnati ta lalubo hanyoyin hadin gwiwa da masu ruwa-da- tsaki a wannan bangare don dakile karuwar yada kalamai masu hadari, “Muna fata gwamnati za ta tashi tsaye ta hanyar hadin gwiwa da masu ruwa-da-tsaki wajen yin duk mai yiyuwa don ganin an kawo karshen yada kalaman batanci. Kada kalaman Mukadashin Shugaban Kasa su zamo an bar su a inda aka yi su kawai, zai yi kyau idan gwamnatin ta yi wani yunkuri don magance wannan matsala,” inji shi.
Cibiyar CITAD ta ce yawancin maganganun batancin da ta gano an yi a kafafen sadarwa na intanet a watan Yulin da ya gabata sun danganci addini da kabilanci, wanda ta ce hakan barazana ce ga zaman lafiyar kasar nan. “Jami’anmu masu bibiyar kafafen sadarwa sun gano cewa a watan Yuli an samu kalaman batanci 601. Mafiya hadari su ne 309 daga ciki, wadanda suka danganci kabilanci, yayin da 202 suka shafi addini. Kamar yadda kowa ya sani wadannan batutuwa biyu suna da muhimmanci a rayuwar dan Adam, kuma suna iya tayar da husuma a kowane lokaci,” inji shi.
Malam Isa Garba ya yi kira ga kafafen watsa labarai su goya wa cibiyar baya wajen yakin da take yi na dakile kalaman batanci ta hanyar hana watsa kalaman batanci ga jama’a.