Majalisar Dattawa ta bankado yadda aka ciri Naira biliyan 7 da miliyan 500 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a asirce.
Majalisar Dattawa ta bukaci Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, su bayyana a gabanta domin warware zare da abawa kan kudaden da aka cira a asirce.
- Ya kashe matarsa mai juna biyu a gadon asibiti
- Gwamnan Edo makaryaci ne —Ministar Kudi
- Ban mutu ba, dogon suma na yi —Ummi Zee-zee
- Budurwar da ta fasa aure saboda Kwankwaso ta samu miji
“Naira biliyan 3.84, Akanta-Janar na Tarayya da Ma’ikatar Kudi ta Kasa ne suka cire su ba bisa ka’ida ba daga CBN… a matsayin rance domin sayen motoci ga jami’an tsaro a 2005 da 2006,” inji Majalisar a wani bangare na rahotonta.
Rahoton binciken da Kwamitin Asusun Gwamnati na Majalisar ya gudanar ya ce an zari kudaden ne a lokuta daban-daban daga asusn Hukumar Kera Motoci ta Kasa daga shekarar 2000 zuwa 2006.
Amma da ta nemin karin bayani daga Darakta-Janar na Hukumar, Aminu Jalal, ya ce ba su da masaniya game da cirar kudaden.
Ya ce Hukumar ta sha rubuta wa Akanta-Janar na Kasa tana neman a dawo mata da kudaden amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.
Da jin haka ne Majalisar Dattawa ta umarci Akanta-Janar din tare da Ministar Kudi, Zainab Ahmed su bayyana a gabanta domin su yi bayani.