Gwamnatin Tarayya ta bayar da tireloli 116 na hatsi domin tallafa wa gajiyayyu da masu karamin karfi a Jihar Bauchi a matsayin tallafin COVID-19.
Ma’aikatar Agaji da Kyautata Rayuwa ta sanar da mika tallafin da aka fitar daga Rumbun Gwamnatin Tarayya bayan amincewa da rabon kayan abincin a Jihar Bauchi.
- Na tara miliyoyi daga sana’a N1,500 a shekara uku
- Matashin ya ba da shanu 50 domin bikin Hanan Buhari
Ministar Ma’aikatar Sadiya Umar Farouk ta ce hatsin da aka bayar sun hada da masara da dawa da kuma gero.
Da yake karbar kayan, Mataimakin Gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da COVID-19 na jihar ya yi alkawarin raba kayan ga wadanda suka cancnata ta yadda ya dace.
Ya kuma yada da yaba da samun tallafin wanda zai taimaka waje rage tasirin da bullar cutar ta haifar wa jama’a.