Gwanmatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Karamar Sallar bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Litinin.
- Amarya ta fasa aure saboda ango ya fadi jarabawar lissafi
- Boko Haram ta sake kai hari Gwoza karo na biyu a watan Ramadan
- Ba ni da alaka da wata kungiyar ta’adda — Abdulsalami
“Laraba 12 da Alhamis, 13 ga Mayu, 2021 su ne ranakun hutun da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin bukukuwan Sallah Karama a bana,” inji sanarwar.
Aregbesola ya taya Musulmin murnar zuwan Sallar, sannan ya kara da kiran ’yan Najeriya a gida da kasashen waje da su dage wajen yi wa kasar addu’ar samun zaman lafiya da karuwar arziki.
Tuni Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar cewa a ranar Talata za a fara neman watan Shawwal na Karamar Sallah.
Ranar Talata 11 ga Mayu 2021, ita ce 29 ga watan Ramadan 1442 Hijiriyya.