Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa cibiyoyi 774 na sabunta layukan waya domin saukaka rajista da kuma samun lambar kasa ta NIN a fadin Najeriya.
Ta kuma amince da tsawaita lasisin kamfanonin sadarwa da ke yin aikin rajistar daga daya zuwa shekaru biyar.
- Jiragen sama ke kai wa ’yan bindiga makamai —Fadar Shugaban Kasa
- Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindiga a Kaduna
- Gwamnatin Gombe ta nada sabon Mai Tangale
Kwamitin hadin gwiwa da Ministan Sadarwa kan hada layukan waya da lambar NIN ne ya sanar da haka a ranar Laraba.
Kwamitin ya kuma ba da umarnin kammala aikin sabon tsarin bayar sa sabbin layukan waya da babu ha’inci a ciki.
“Wannan zai tabbatar da cewa ba a maimaita abin da aka yi a baya ba wanda aka samu matsala ta hanyar rajista da wasu wakilai”, inji sanarwar kwamitin.
Sanarwar ta ce, “An amince da tsawaita wa’adin lasisin rajistar NIN na wakilcin daga shekara 1 zuwa 5 ne bayan gamsuwa da aikin kamfanonin kuma za ci gaba da sa ido a kan.
“Wannan yunkurin gwamnati ne saukaka yin rajista ga yan Nijeriya da kuma halastattun baku,’’ inji sanarwar.