Kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa mai nazari kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata, zai sake zama a mako mai zuwa domin ci gaba da tattauna batun mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da mambobin Ƙungiyar Ƙwadago NLC suka fice daga tattaunawar da suka soma a ranar Larabar da ta gabata.
- Jami’an tsaro sun kai samame kan masu sayar da raguna a Legas
- Jemagu: Garin da maza ba su auren macen da ta wuce sakandare a Kano
Sai dai a ckin wasiƙar gayyatar da shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya aike wa mambobin kwamitin a matakan jihohi, ya ce kwamitin ya amince da sauya matsayarsa kan naira 48,000 da ya ɗauka ranar Larabar.
Wasiƙar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon da su gayyaci mambobinsu domin halartar zaman da za a yi ranar Talata 21 ga watan Mayu.
Tun da farko dai ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, lamarin da ya sa tunaninsu da na kwamitin ya yi hannun riga.
A nasu ɓangare, kamfanoni masu zaman kansu sun amince da naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.
Aminiya ta ruwaito cewa ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun ce sun fice daga tattaunawar ta ranar Laraba ne saboda sun fahimci cewa gwamnatin ƙasar ba da gaske ta yi ba.
A Larabar makon jiya ce NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.
Mambobin ƙungiyar ta NLC sun bayyana mamaki kan dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.
Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000.
Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawarta kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.
Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu gamsassun hujjoji da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.