Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gwangwaje Gwarzuwar Musabakar Alkur’ani ta Kasa, Aisha AbdulMutalib, kyautar sabon gida da kuma kujerar aikin Hajji.
An dai gudanar da gasar ce a Jihar Sakkwato.
- Ku ji tsoron Allah a alkawuranku —Farfesa Lugga ga ’yan takarar gwamnan Kastina
- A watan Maris za a fara hako man fetur a Jihar Nasarawa – NNPC
Gwamnan ya jinjina wa gwarzuwar wacce ’yar asalin Karamar Hukumar Potiskum ce da ke jihar, inda ya ce ta fitar da jihar kunya a idon duniya.
Mai Mala ya kuma sanar da nadin Aishan a matsayin Jakadiyar Harkokin Alkur’ani ta jihar, sannan ya kara mata da kujerar aikin Hajji ita da maigidanta.
Kazalika, Gwamnan ya amince da bayar da kujerar Hajjin ga jami’an da su ma suka yi mata rakiya zuwa wajen gasar a Sakkwato.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ingantaccen ilimin boko da na islamiyya a ga ’yan Jihar, yana mai cewa a matsayinsu na wani yanki na tsohuwar Daular Borno, Yobe na da dadadden tarihin ilimin addinin Musulunci.
Gwamnan ya kuma sanar da sanyawa sabuwar kasuwar garin Nguru sunan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar, Shehu Gibrima.