✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Sakkwato ya gwangwaje ma’aikata da goron Sallah

Daga ranar Alhamis ’yan fansho da sauran ma'aikatan jihar Sakkwato za su fara jin 'alat' din kudaden goron Sallah daga

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto, ya ba da umarnin da fitar da kudi domin bayar da goron sallah ga dukkan ’yan fansho da ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi domin bikin Sallar Layya.

Goron sallar, gwamna ya raba shi gida biyu, ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi za a ba su dubu 30 kowanensu.

Masu karbar fansho ds ma’aikatan hukumar lafiya matakin farko za su amfana da dubu 20 suma don shagalin sallah.

Wannan kyautar za a fara biya ne daga ranar Alhamis 13 ga watan Yuni 2024.

Gwamnan ya roki Allah Ya sa a yi shagalin sallah lafiya a jiha da kasa baki daya.