✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Ribas ya rantsar da Kwamishinoni kwana 2 da shiga ofis

Shi ne Gwamna na farko da ya nada Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya rantsar da sababbin Kwamishinoni kwana biyu bayan rantsar da shi.

Sabon Gwamnan dai ya bukace su dauki nadin nasu a matsayin wata gagarumar dama ta nuna kishin kasa tare da hdimta wa mutanen Jihar. Mutum hudu ne dai Gwamnan ya rantsar.

Wadanda aka rantsar din sun hada da Farfesa Zacheous Adango (Ma’aikatar Shari’a), Dokta Alabo George Kelly (Ma’aikatar Ayyuka), Farfesa Chinedu Mmom (Ilimi) da kuma Barista Isaac Kamalu (Kudi).

An rantsar da su ne a farfajiyar Majalisar Zartarwar Jihar da ke Gidan Gwamnatin Jihar a Fatakwal, babban birnin jihar ranar Laraba.

Dukkan mutum hudun da ya nada dai sun yi aiki da gwamnatin Gwamnan Jihar da ya gabata, Nyesom Wike.

Kazalika, Gwamnan ya rantsar da Dokta George Nweke a matsayin Shugaban Ma’aikatan Jihar, sai kuma Ibierembo Thompson wanda aka nada mamba a Hukumar Zabe ta Jihar (RSIEC).

Daga cikin Gwamnoni 28 din da aka rantsar dai ranar Litinin, Gwamnan na Ribas ne kadai ya kai ga rantsar da Kwamishinoni. Sai dai wasu daga cikinsu sun nada hadimai.