✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Oyo ya rufe kamfanin hakar ma’adinan ’yan China

Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya bayar da umarnin rufe wani kamfanin hakar ma'adinai mallakar wasu ’yan kasar China a jiharsa.

Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya bayar da umarnin rufe wani kamfanin hakar ma’adinai mallakar wasu ’yan kasar China a jiharsa.

Da yake bayar da umarnin a lokacin da ya ziyarci kamfanin a ranar Asabar, gwamnan ya ce tun farko Gwamnatin Tarayya ce ta ba wa kamfanin lasisin sarrafa tayoyin mota da batura, amma aka mayar da shi wurin hakar ma’adinai.

“Idan kun lura babu taya ko batir ko daya a cikin wannan wuri sai abubuwan da suka danganci hakar ma’adinai kawai,” in ji shi a harabar kamfanin da ke garin Idi-Ayunre a Karamar Hukumar Oluyole.

Gwamna Makinde ya tabbatar cewa an kama wasu ma’aikatan kamfanin hudu kuma za a gurfanar da su gaban kotu kan laifin hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya a jihar.

Binciken Aminiya ya gano cewa gwamnatin jihar ta fara daukar tsauraran matakai a wuraren hakar ma’adinai tun daga lokacin da wani abu ya fashe a cikin wani gida a Ibadan wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da hasarar kadarori.

Matakan da gwamnati ta dauka bayan fashewar sun hada da dakatar da wani basarake na garin Ido, Oba Gbolagade Muritala Babalola, da aka zarge shi da hannu wajen hulda da masu hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya.

Haka kuma an kama wasu mutane uku a cikin wani gida a Ibadan da aka gano abubuwan fashewa a cikinsu.