✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Oyo ya kaurace wa bikin bude ofishin yakin zaben Buhari a Ibadan

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Cif Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Jihar Abiya Dokta Orji Uzor Kalu da Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole sun nemi Shugaba…

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Cif Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Jihar Abiya Dokta Orji Uzor Kalu da Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya hanzarta daukar matakin sasanta tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Ministan Sadarwa Barrister Adebayo Shittu, wadanda gabar siyasa a tsakaninsu ta sa Gwamna Ajimobi ya ki halartar bikin bude ofishin yakin neman sake zaben Shugaba Buhari da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a birnin Ibadan.

A maimakon halartar wajen wannan bikin, Gwamna Ajimobi tare da kusoshin Jam’iyyar APC a Jiha Oyo, wani gangamin taro suka yi daban a daidai wannan lokaci da ake gudanar da bikin bude ofishin yakin neman zaben na Shugaba Buhari.

Kamar yadda Aminiya ta binciko, wata mummunar gabar siyasa da ke tsakanin Gwamna Ajimobi da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu ce ta haifar da rabuwar kawunansu, wanda ya yi sanadiyyar suka shirya muhimman taro biyu na APC a cikin gari daya kuma a lokaci daya.

Cif Ken Nnamani da Dakta Orji Uzor Kalu da Farfesa Isaac Adewole da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a sashen Kudu maso yamma, Cif Pius Akinyelure da Kodineta na gangamin yakin sake zaben Buhari da Osinbajo, Alhaji Usman Ibrahim suna daga cikin jiga-jigan APC na kasa da suka halarci bikin bude babban ofishin da zai yi wa Shugaba Buhari kamfe a sashen Kudu maso yamma, domin sake tsayawa takarar shugabancin kasa a badi.

Minista Shittu, wanda ya nuna sha’awar tsayawa takarar Gwamna a zabe mai zuwa a Jihar Oyo, shi ne ya jagoranci bikin bude wannan ofis. Rashin ganin Gwamna Ajimobi da mukarrabansa a wajen bikin ne ya sa Cif Nnamani da Dokta Kalu suka yi wannan kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun da su hanzarta daukar matakin yin maganin wannan gabar siyasa a tsakanin gwamnan da Minista tun kafin al’amarin ya kazance.