Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, inda ya tafi kasar waje hutun neman lafiya na kwana 21.
A cikin wata wasika da ya aike wa da Majalisar Dokokin Jihar ranar Talata, Gwamnan ya ce Mataimakin nasa zai rike kujerar a matsayin mukaddashi har lokacin da zai dawo.
- Tinubu na ganawa da Akpabio da Jonathan a Aso Rock
- Kundin Adana Tarihi na Guinness ya tabbatar da bajintar Hilda Baci
Kakakin Majalisar, Oladimeji Oladiji, wanda ya karbi kwafin wasikar ya ce hutun Gwamnan zai kare ne ranar 6 ga watan Yulin 2023.
A cewar Kakakin, “Hutun, wanda ya fara ranar 7 ga watan Yuni, za a ci gaba da shi har zuwa ranar 6 ga watan Yulin 2023, saboda ranakun hutun da za a samu na Ranar Dimokuradiyya da kuma na Sallah Babba.
“Mataimakin Gwamna, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa ne zai rike masa ragama har zuwa lokacin da zai dawo ranar 6 ga watan Yulin 2023,” in ji wasikar.
A baya-bayan nan dai Gwamnan ya sha fama da rashin lafiya inda ba a cika ganinsa a wuraren taruka da ayyukan gwamnati ba a kai a kai.
Mutane dai sun yi ta korafi a kan haka, kodayake hadimansa sun sha musantawa, inda suka ce lafiyarsa kalau. Amma daga baya sun amince cewa yana fama da rashin lafiya.