Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya bada lamunin bude wuraren ibada, otal-otal, wuraren kasuwanci da kuma wuraren shakatawa da ke jihar.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Jihar Kunle Simon, ya fitar a ranar Laraba.
- An kara ranakun fita a jihar Ogun
- An sake tsawaita dokar kulle a Ogun
- An bullo da sabuwar hanyar gwajin Coronavirus a Ogun
- ’Yan sanda sun cafke mata da miji da kan mutum a Ogun
Sanarwar ta ce “Mun yi hakan ne saboda yadda muka ga ana samun karancin samun masu kamuwa da cutar Coronavirus, amma duk da haka za mu ci gaba da yin gwajin cutar a wuraren da aka tanadar.”
“Sannan muna umartar jama’a da su ci gaba bin matakan kariya da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta bayar.”
Duk da cewar ana ci gaba da samun wanda suke kamuwa da cutar ta Coronavirus a fadin Najeriya, amma tasirinta ya ragu, wanda hakan ne ya sanya gwamnatocin jihohi da dama bude Kasuwanni, Makarantu, wuraren ibada da sauran wurare na gudanar da al’amuran yau da kullum tare da kafa sharadin bin matakan kariya.
Tun a watan Maris ne dai Gwamna Abiodun ya kulle wuraren ibadar yayin da annobar COVID-19 ta barke a fadin Najeriya, inda a watan Agustan da ya gabta ya bude wasu daga cikin wuraren na ibada da makarantu.