Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya yi Allah-wadai da matakin da direbobin manyan motoci suka dauka na rufe wasu hanyoyi a Jiharsa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’arsa mai kula da hulda da ’yan jarida, Mary Noel Berje, ta fitar.
- Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar rugujewa – Sanusi
- Abin da ya hada ni da Adam A. Zango —Ummi Rahab
Gwamna Bello, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ja kunnen direbobin da su guji daukar doka a hannunsu.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ba da rahoton yadda wasu matafiya suka kwashe kusan sa’a 24 a Bida bayan da direbobin suka rufe hanyar Bida zuwa Lambata da Bida zuwa Minnā da Bida zuwa Mokwa don nuna takaici da yadda hanyar ta lalace.
Hanyar ce dai ta hada kudanci da arewacin Najeriya.
Direbobin sun kuma bukaci Gwamnatin Jihar Neja ta kyale su su yi amfani da hanyar Minnā zuwa Bida, wadda yanzu haka kamfanin Dantata & Sawoe ke ginawa.
Gwamnan ya ce ko da yake direbobin suna da hurumin gudanar da zanga-zangar lumana, abin da suka yi ya take hakkin sauran jama’a.
“Shawarar direbobin ta rufe hanya ta saba doka, kuma hakan ba zai razana gwamnatin Jiha ta kyale su su yi amfani da hanyar Minna zuwa Bida, wadda mallakar jiha ce, ba”, inji shi.
Gwamna Bello ya kuma umarci Ma’aikatar Ayyuka da Samar Ababen More Rayuwa ta Jihar Neja ta tuntubi jami’in Ma’aikatar Ayyuka ta Kasa a Jihar don zakulo hanyar daukar matakan gyara sassan da suka lalace a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Lapai zuwa Bida.
Daga nan gwamnan ya yi kira da a kwantar da hankali duk da tsananin da aka jefa ’yan kasa da ba su ji ba, ba su gani ba.