Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya sanar da sauke Sakataren Gwamnatinsa Tijjani Ahmed Aliyu.
Sauke Sakataren na Gwamnatin Jihar Nasarawa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da take dauke da sa hannun Babban Sakataren Gudanarwa na Gidan Gwamnatin Jihar Hamza Abubakar Gayam.
Sanarwar ta yi godiya ga Sakataren Gwamnatin da aka sauke tare da umurtar sa ya mika dukkanin kayayyakin gwamnati da suke hannunsa ga Babban Sakataren Harkokin Gwamnati a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Mu’azu Adamu Gosho.
Idan ana iya tunawa dai a makon jiya ne Majalisar dokkokin Jihar ta bukaci Gwamnan na Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya kori Sakataren Gwamnatinsa Tijjani Ahmed Aliyu bayan wani binciken kwamitin majalisar na mussamman ya gano tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar na da hannu a wata badakalar kwangila ta naira miliyan 248.4 a ma’aikatar ilimin jihar a tsohuwar gwamnatin da ta shude ta tsohon Gwamna Umar Tanko Al-Makura.
Tun dai bayan mika wannan bukata ta majalisar dokokin jihar ake ta samun rade-radin cewa tsohon Sakataren ya yi murabus.