Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya kawo sauke daukacin masu mukamai na siyasa a gwamnatinsa.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na jihar da aka yi a gidan gwamnati, a ranar Alhamis.
- Shugaban karamar hukuma ya rasu ana dab da rantsar da shi a Yobe
- Buhari ya yi bakin kokarinsa, ya kamata ya huta —Garba Shehu
Sule ya gode wa wadanda hakan ya shafa bisa yadda suka taimaka wa gwamnatinsa wajen cimma nasarorin da ta samu a cikin shekaru hudu da suka gabata.
“Da farko ina godiya ga kowa da kowa da kuka samu damar zuwa wannan taron.
“Wannan shi ne karo na karshe da muka yi irin wannan taro, lokacin da muka gayyace ku don neman ku yi duk abin da ya dace don ganin mun samu nasara a zaben da ya gabata.
“Na ga yadda kuka yi aiki kamar babu gobe domin mu samu nasara a zabe.
“A karshe duk mun yi nasara saboda mun lashe zabe,” in ji shi.
Ya yi alkawarin sake yin aiki tare da sabbin wadanda aka nada sannan ya tabbatar da amincinsu, gaskiyarsu da kuma kwazonsu.
Da yake jawabi a madadin wadanda aka nada, tsohon Atoni-Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Alhaji Abdulkareem Kana, ya gode wa gwamnan da ya zabe su don su yi aiki bisa cancanta.
Kana ya yi addu’ar Allah Ya yi masa jagora, gabanin rantsar da shi a karo na biyu.