✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Nasarawa AA Sule ya yi tazarce

Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya yi nasarar komawa kan kujerarsa bayan zaben da aka kammala ranar Asabar.

Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya yi nasarar komawa kan kujerarsa bayan zaben da aka kammala ranar Asabar.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa AA Sule ya yi nasara ne bayan ya ba wa babban abokin hamayyarsa,  David Umbugadu na jam’iyyar PDP, tazarar kuri’u 62,000.

Baturen zaben kuma Shugaban Jami’ar Jos, Farfesa, ya sanar cewa Gwamna Abduulahi A Sule na APC, ya samu kuri’u 347, 209 a yayi n da Umbugadu ya samu  283,016.

Kananna hukumomin da AA Sule ya lashe su ne: Wamba, 12, 124; Keana, 9, 598; Toto, 15, 787; and Keffi, 27,737; Nassarawa, 27,992 ; Awe, 26, 966; 28, 322; da kuma Lafia, 107, 213.

A daya bangaren kuma, dan takarar PDP ya samu 23,787 a Akwanga;  Doma, 19, 737; Nassarawa Eggon, 36, 825; Kokona, 19, 045; and Obi, 29, 467; Karu, 46, 565.