✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Legas na ganawa da Buhari kan EndSARS

Gwamnan Jihar Legas na Fadar Shugaban Kasa domin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari kan rushe sashen ‘yan sanda na SARS mai yakar ayyukan fashi. Ziyarar…

Gwamnan Jihar Legas na Fadar Shugaban Kasa domin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari kan rushe sashen ‘yan sanda na SARS mai yakar ayyukan fashi.

Ziyarar gwamnan na zuwa ne ‘yan awanni bayan ya halarci taron zanga-zangar a jiharsa, inda ya yi alkawarin gabatar da bukatunsu ga Shugaban Kasa.

A lokacin ganawar, Sanwo-Olu ya yi alkawarin gidauniyar miliyan N200 domin biyan diyya ga wadanda lamarin ya yi ajalinsu a jihar.

Ya yi alkawarin tabbatar da ganin wadanda aka zalunta sun samu adalci sannan ya ba da umarnin a saki dukkannin mutanen da aka tsare saboda zanga-zangar.

%d bloggers like this: