Gwamnatin Legas za ta gina wani sabon filin jirgin sama a yankin Lekki, wanda zai zama na biya a jihar bayan filin jirgi na Murtala Mohammed.
Kakaki na musamman ga gwamnan jihar, Ope George, ya ce Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta samu amincewar Gwamnatin Tarayya kan gina sabon filin jirgin a jihar.
- Manyan motoci sun tare hanyar Abuja kan rufe masana’antar Dangote
- Kotu ta yanke wa masu garkuwa da mutane daurin shekara 36
Batun gina filin jirgin saman jihar ya tsaya cik tsawon shekaru, tun lokacin da aka gabatar da ia a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Babatunde Fashol.
A lokacin an tura wa masu zuba jari a fadin duniya takardun bukatar su zuba jari a aikin filin jirgin da aka kiyasta zai lakume Dala miliyan 450 a lokacin.
An tsara aikin gina filin jirgin ne a matsayin hadin gwiwa tsakanin ’yan kasuwa da gwamnatin jihar, wadda za ta samar da filin da sauran kayan more rayuwa.
A daya bangaren kuma, masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya, za su gina filin jirgin a karkashin tsari mai gamsarwa kuma daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya.
A baya wasu manyan kamfanonin kwararru hudu sun yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Legas a matsayin masu ba da shawara kan aikin filin jirgin.
Sai dai duk da haka ba a aiwatar ba, sai yanzu da Gwamnatin Sanwo-Olu ke shirin aiwatarwa da zummar filin zai karbi fasinjoji milian biyar a shekara.
Hadimin gwamnan ya ce aikin da ake sa ran za a fara a shekarar 2023, za a gina shi ne a kan fili mai fadin kadada 3,500, kuma tuni an riga an kammala zanen tsari da na’urorin jiragen sama.
A gefe guda kuma ana ci gaba da nazari kan dabaru, yadda za a samu kudade da sauran batutuwa, wadanda bayan su za a fara batun kasuwanci.