Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ba da umarnin a kama wani soja da ya hango da kansa ya taka dokar amfani da hanya a kan babur dinsa.
Rahotanni sun ce Gwamnan tare da tawagarsa ne suka bi sojan har cikin barikin sojoji da ke kusa da sansanin Ozumba Mbadiwa Bonny a birnin na Legas.
- An cafke matasa 6 kan zargin satar kayan kida a coci
- Kotu ta tsare matashi kan zargin luwadi da yaro mai shekara 11 a Kano
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Legas ta haramta sana’ar acaba da babura a wasu Kananan Hukumominta, ciki har da Iru/Victoria Island, inda a nan ne al’amarin ya faru.
Kodayake dai dokar haramcin amfani da babur din ba ta shafi jami’an tsaro ba, amma saba dokar hanya da sojan ya yi ne ya ja hankalin Gwamnan da har ya bukaci a kamo shi.
An ga Gwamnan tare da tawagarsa cikin wani bidiyo da ya karade gari sun sauka daga motocinsu inda suka tunkari sojan kan laifin da ya aikata.
A nan ne aka ce Sanwo-Olu ya bukaci a kama sojan tare da kwace babur din nasa.
Ko a shekarar 2012, zamanin mulkin Gwamna Babatunde Fashola, makamancin wannan ya faru, inda Gwamnan ya sa aka damke wani babban jami’in soja bisa laifin yin tuki a hanyar motocin safa-safa.