✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

"Yan sanda a halin yanzu suna binciken al'amuran da suka shafi mutuwar matar."

An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas.

Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas.

“Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas kuma likitocin jami’ar UNILAG sun tabbatar da mutuwarta a gaban rundunar  ’yan sanda daga sashin Sabo,” kamar yadda sanarwar a wani ɓangare ta bayyana.

Hundeyin ya ci gaba da cewa, an kai gawar zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin cututtuka masu yaɗuwa da ke yankin Yaba a jihar domin adanawa.

Ya ƙara da cewa “Yan sanda a halin yanzu suna binciken al’amuran da suka shafi mutuwar matar.”