✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#BugaChallenge: Yadda Shugabar Hukumar ’yan Najeriya mazauna ketare ta cashe

Wakar Buga, wadda Kizz Daniel ya yi, tana tashe a yankin Afirka da sauran sassan duniya, musamman a kafofin sada zumunta

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasasehn Ketare, Abike Dabiri, ta  bi sahun masu fada aji da suka wallafa bidiyonsu suna rawar shahararriyar wakar nan ta Buga, wadda ke tashe a duniya.

Wakar Buga, wadda mawakin Kudancin Najeriya, Kizz Daniel ya yi, ta zamo abar yayi a Afirka da sauran sassan duniya, musamman a kafofin sada zumunta.

Abike dai ita ce ta saki nata bidiyon a karshe daga wannan jeri, kuma ta wallafa bidiyon ne a shafinta na Instagram.

“Taronmu da mata masu girma wato Kungiyar Lauyoyi Mata ’Yan Afirka ke nan, tare da shugabar kungiyar reshen Najeriya, inda na gabatar da jawabi.

“Bayan kammalawa, mai gabatar da masu jawabai, Charles Ajiboye, ya kalubalance ni da na yi rawar Buga, kuma ina tunanin na lashe kambu da wanann taku nawa”, in ji ta.

Wannan salon gasa da ake wa take da #BugaChallenge, an fara ne a kafafen sada zumunta, tun daga fitowar wakar watanni da suka gabata.

Manyan mutane da dama a Najeriya da sauran yankin Afirka dai na ta karade kafafen da bidiyon rawar wakar.

Daga cikinsu akwai dai Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da na Kogi Yahaya Bello da mataimakinsa da su ma su ka yi wannan rawa a lokuta daban-daban.

Daga kasashen ketare akwai da irinsu Shugaban Kasar Laberiya, George Weah, da aka ce shi ne ya lashe kambun iya takun wakar a kasar ta yanar gizo.

Sai kuma minista mafi karancin shekaru ta Kenya, da ita ma ta yi a wani taron kasar da aka gudanar.