Dadewar shugaban Laberiya George Weah a kasashen waje ya sa ‘yan kasar shiga cigiyarsa, da jefa masa maganganu a shafukan sada zumunta na intanet
Shugaban Laberiya ya bar kasar ne zuwa wasu jerin kasashen waje tun cikin watan Oktoba domin halartar tarukan siyasa, sannan ya zarce Qatar gasar cin kofin duniya don kallon dansa da ke buga wa Amurka wasa.
- Buhari zai tafi Liberia ranar Talata
- Zanga-zanga kan sanya Hijabi: Iran ta dakatar da ayyukan ’yan Hisbah a kasar
Tsawon watannin da tsohon dan kwallon ba ya kasar tasa ta haihuwa, inda talakawa ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma karancin su, ya sa sun soma kokawa.
Weah ya yi ta saka hotunansa da dansa a Qatar a shafinsa na Twitter yana mai alfahari da nasarar da ‘yan wasan Amurka ke samu, na kai wa mataki na gaba a gasar.
Sai dai hotunnan jin dadi da sharholiyar ba su yi wa yawancin ‘yan kasar dadi ba, la’akari da yadda suke fadar albarakacin bakinsu a shafukan sada zumunta.
“Wannan ba al’ummar Laberiya ya ke yiwa aiki ba, ganin yadda ya bar kasar nan ya tare da dan sa,” inji wani mai suna Momo Fully.
Wani dan jam’iyyar adawa na zargin Weah da dora kasar a ‘keken bera’ da yawan tafiye-tafiyensa.
A watan Nuwamba ne Weah ya tsawaita zamansa a kasashen waje, wanda hakan ta sa zaman ya kasance mafi tsawo tun da ya zama Shugaban Kasa.
Weah ya zama Shugaban Kasar a shekarar 2017 da alkawarin zai yaki talauci da cin hanci da rashawa, ‘yan adawa sun ce bai cika alkawarin da ya dauka wa talakawa ba.
Ana sa rai zai dawo kasar a ranar 18 ga watan Disamba mai zuwa.