✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kuros Riba, Ayade ya koma APC

Shugaban Kwamitin Rikon APC na Kasa, Mai Mala Buni ne ya karbi Gwamna Ayade.

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Rikon APC, Mamman Mohammed ne ya sanar da sauya shekar Ayade a safiyar Alhamis.

“Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya karbi Gwamnan Kuros Riba, Dokta Ben Ayade wanda ya dawo jam’iyyar daga PDP,” inji sanarwar da ya fitar.