Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya kori kwamishinan noma, Mista David Apeh daga aiki.
Har wa yau, gwamnan ya kori mataimakinsa na musamman kan harkokin agajin gaggawa, Mista Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu, shugabar hukumar kula da yawon bude ido ta jihar.
- An tantance mutum miliyan 1 don yin aikin kidaya —NPC
- Mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara
Korar tasu na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Ayoade-Arike, ta fitar a Lokoja.
Ko da yake ba a bayyana dalilin da ya sa gwamnan ya sallame su daga aiki ba.
Sai dai ta ce an sallami Isah-Yunusa da Salifu daga aikinsu ne saboda rashin da’a.