✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Kebbi ya sallami mukarrabansa daga aiki

Rusa Majalisar Zartarwar Jihar Kebbi ta fara aiki nan take

Gwamnan  Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya rusa Majalisar Zartarwar jihar ba tare da bata lokaci ba.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Babale Yauri.

Yauri, ya ce rushe Majalisar Zartarwar Jihar ya fara aiki ne nan take daga ranar Laraba, 7 ga Satumba, 2022.

A cewar sanarwar, “Gwamnan yana matukar godiya da irin gudunmawar da kowane mamba na Majalisar da aka rusa tare da gode musu bisa jajircewarsu wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar a tsawon lokacin da suke rike da mukama gwamnatin jihar.”

Gwamnan ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a nada mambobin majalisar zartarwar jihar, ya kara da cewa gudunmawar da mambobin majalisar da aka rusa suka bayar abin yabawa ne.