✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Gombe ya zama sabon shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa

Zai karbi ragamar kungiyar daga Gwamnan Filato, Simon Lalong

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya zama sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NGF).

Hakan ya biyo bayan zaben da kungiyoyin ta gudanar a ranar Talata.

Inuwa, wanda aka zaba a wa’adin farko a matsayin Gwamnan Gombe a shekara ta 2019, ya sake lashe zaben a karo na biyu a zaben 2023 da aka kammala a watan Maris.

Zai karbi ragamar shugabancin kungiyar ne daga Gwamnan Filato mai barin gado, Simon Lalong, bayan ta shafe shekara hudu yana jagorancin ta.