✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya wa Gadar Neja ta 2 da Buhari ya gina sunansa

Buhari ne dai ya gina gadar kuma ya kaddamar da ita ranar Talata

An sanya wa Gadar Neja ta Biyu, wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gina a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya kuma kaddamar da ita ranar Talata sunansa.

Hadimin Shugaban a fannin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Talata.

A cewarsa, “Ya ku maza da mata, yanzu a hukumance ta tabbata an sanya wa gadar Neja ta Biyu sunan Muhammadu Buhari.”

Kazalika, shi ma Hadimin Buharin a kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi, shi ma ya tabbatar da labarin a shafin nasa na Twitter.

Sai dai ya ce sanya sunan kawai zai tabbata ne bayan amincewar Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

“Tare da amincewar Gwamnoni da saura masu ruwa da tsakin yankin Arewa maso Gabas, yanzu za a rika kiran gadar da sunan Muhammadu Buhari,” kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na Twitter.