✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Gombe ya bukaci maniyyatan Jihar su yi mata addu’a a Saudiyya

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi kira ga maniyyatan Jihar da cewa su zama jakadu na gari su kuma sanya Jihar da…

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi kira ga maniyyatan Jihar da cewa su zama jakadu na gari su kuma sanya Jihar da Najeriya cikin adduo’insu.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake yi wa maniyatan na bana jawabin bankwana a lokacin da suke shirin fara tashi zuwa kasa mai tsarki don gudanar da Aikin Hajjin bana.

Ya ja hankalin maniyyatan da su nesanta kansu daga duk wani abu da zai iya bata musu aikin Hajji, ko taba mutuncinsu ko na Jihar da suka fito.

Ya tunatar da su cewa, “Ku Sani kasar Saudiya ba kamar Najeriya ba ce, doka tana aiki ba sani ba sabo kan duk wanda aka kama da aikata laifi ko rashin gaskiya.”

A cewarsa, gwamnati ta himmatu wajen ganin alhazan jihar sun yi aikin Hajji cikin natsuwa inda ya ce za a fara ba su kulawa tun daga Najeriya har zuwa kasa mai tsarki.

“Najeriya tana fuskantar kalubale iri-iri, ku jajirce da addu’a don neman sauki wa al’ummar kasar,” in ji shi.

Shi ma Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Gombe, kuma Sarkin Dukku, Alhaji Haruna Abdulkadir Rasheed, yaba wa Gwamnan ya yi bisa jajircewarsa na ganin an gudanar da Aikin Hajji na bana cikin nasara.

Ya ja hankalin alhazan jihar da su mayar da hankali ga ibada maimakon saye-sayen tsaraba tun kafin gabatar da ibadar tasu.

Shi ma da yake tsokaci, Sakataren Hukumar Jindadin Alhazan Jihar, Alhaji Sa’adu Hassan, yabawa Gwamna Inuwa Yahaya ya yi bisa samar da masaukan alhazai masu kyau a can kasa Mai tsarki

Ya ce da farko jirgi mai daukar alhazai 350 aka tsara zai yi jigilar alhazan Jihar, amma bisa jajircewar Gwamnan yanzu an samar da jirgi mai daukan mutum 550 da zai tashi da sawun farko na maniyyatan jihar.

Yace bayan tantance maniyyatan da aka lika sunayensu, za a fara jigilar mahajjatan gadan-gadan a ranar Laraba.

A bana dai, ana sa ran maniyyata 2,556 ne za su sauke farali a Hajjin bana daga Jihar.