✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi ya zama mashawarcin Gwamnan Filato kan wasanni

Mikel Obi ya zama mai ba Gwamnan Filato shawara kan harkokin wasanni.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nada shahararren dan wasan kwallon kafa Mikel Obi, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin wasanni.

Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun daraktan watsa labaran gwamnan, Gyang Bere ce ta bayyana haka.

Har ila yau sanarwar ta ce gwamnan ya amince da nada Honarabul Sunday Samuel Amuna, a matsayin shugaban hukumar makarantun matakin farko ta Jihar (SUBEB).

Ya kuma nada Akitet Hart Bankat a matsayin Janar manajan Hukumar bunkasa garin Jos da kewaye (JMDB) da kuma Farfesa Christopher Sabo Yilgwan, a matsayin Shugaban Asibitin Filato.