Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya sauya sheka daga jam’iyyarsa PDP zuwa APC mai mulki a tarayya.
Mista Umahi ya sauya sheka ne a ranar Talata tare da mukarraban gwamnatinsa.
Umahi wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas ya ce shugabancin jam’iyyar PDP ya zaluncin.
Sauya shekar tasa na zuwa ne bayan rade-radi da kuma taron kusoshin jam’iyyar APC na kasa daga ranar Litinin har zuwa safiyar Talata.
Gabanin ficewar gwamnan daga PDP an yi ta zargin zai bar ta ne saboda APC na shirin ba shi tikicin takarar Shugaban Kasa a 2023.
Ba takara ba ce burina —Umahi
Sai dai ya ce barinsa PDP ba shi da alaka da fitar da dan takarar Shugaban Kasar APC daga yankin ko ba shi tikitin tsayawa takarar.
Ya ce komawar tasa APC za ta fi ba shi damar yin aiki kafada-da-kafada da yankim aiki fiye da jam’iyyar PDP.
Har’ila yau ya ce ya koma sabuwar jam’iyyar ce a matsayin sadaukar da kai domin amfanin ‘yan kabilar Ibo, wadanda ya ce shi mai rajin nema musu jin dadi ne ko ba ya kan mulki.
“Ina fada da babar murya cewa ban nemi tikicin takarar Shugaban Kasa a PDP ba kuma ba zan nema ba; duk wanda ya ce na bar ta ne saboda ta ki ba ni tikici sokiburutsu kawai yake yi.
“Ko da
“APC ba ta yi min ko yankin Kudu maso Gabas alkawarin mukami ba amma na yi sauya sheka ne a matsayin bijire wa zaluncin da PDP ke ta yi a yankin daga 1999 zuwa yanzu”, inji shi.
Ya ce tun 1999 yankin ke yin PDP amma har yanzu jam’iyyar ba ta ga dacewar tsayar da dan takarar Shugaban Kasa daga yankin ba, wanda ya ce ke da mutanen da suka cancanci su jagoranci Najeriya.