✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Delta ya yi wa ’yan kwallon Eagles ruwan Naira

A ranar Litinin da ta wuce ce Gwamnan Jihar Delta Mista Ifeanyi Arthur Okowa ya ba kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kyautar Dala dubu…

A ranar Litinin da ta wuce ce Gwamnan Jihar Delta Mista Ifeanyi Arthur Okowa ya ba kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kyautar Dala dubu 60 (kimaniin Naira miliyan 21 da dubu 660).

Gwamnan ya ce ya yi haka ne saboda jin dadin yadda kungiyar ta lallasa Seychelles a wasan karshe na neman hayewa gasar cin Kofin Duniya.  Gwamnan ya ce ya yi farin cikin yadda kungiyar ta samu hayewa gasar cin Kofin Afirka bayan ta yi kunnen doki 1-1 da kasar Afirka ta Kudu a bara.  Haka kuma Gwamnan ya yaba da yadda kungiyar ta lallasa kasar Masar a wasan sada zumunta da aka yi a ranar Talatar da ta wuce bayan kungiyar ta shafe kimanin shekara 29 rabon da ta doke kasar Masar a kowane wasa.

Wannan da wasu dalilai na daga cikin abin da ya ja hankalin Gwamnan wajen saka wa kungiyar Super Eagles.

Sai dai a kyautar an nuna Kocin kungiyar Gernot Rohr zai tashi da Dala dubu 10 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 610), yayin da sauran ’yan kwallon za su tashi da ragowar Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan 18 da dubu 50).

Kafar labaran wasanni ta Intanet ta Thenff.com ta ce Gwamnan ya yi haka ne don ya ci gaba da karfafa wa ’yan kwallon gwiwa musamman wajen tunkarar gasar cin Kofin Afirka wanda zai gudana a Masar a watan Yuni mai zuwa.

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta yaba wa Gwamnan game da wannan karamci da ya yi wa kungiyar kamar yadda ta yaba wa Ahmed Musa, dan kwallon Super Eagles game da kyautar Naira miliyan 4 da ya ba kungiyar kwallon kafa ta U-23 a ranar Litinin da ta wuce saboda lallasa Libya da ci 4-0.