✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan CBN ya sayi fom din Takarar Shugaban Kasa a APC

Ya sayi fim din kan Naira miliyan 100

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emiefele ya bi sahun takwarorinsa masu neman takarar Shugabancin Kasa a karkashin jam’iyyar APC bayan sayen fom a kan Naira miliyan 100.

Ya dai sayi fom din ne ranar Juma’a a hannun Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyar a cibiyar taro ta kasa da ke Abuja.

Emiefele tun shekara ta 2014 tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nada shi Gwamnan Babban banki, bayan tube Sunusi Lamido Sunusi.

Tsohon shugaban bankin Zenith, Emefiele a shekara ta 2019 ya kafa tarihi a matsayin Gwamnan CBN da ya rike mukamin har sau biyu.