Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa.
Hukuncin Kotun Daukaka Karar ya yi watsi da wanda Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan ta yanke a baya da ya soke zaben gwamnan.
Alkalan kotun su biyar karkashin jagorancin Mai Sharia’a Adzira Mshelia, sun yi ittifaki wajen tabbatar da nasarar gwamnan da jam’iyyarsa ta PDP a zaben, bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar musu.
Da yake karanta hukuncin da alkalan suka yanke, Mai Shari’a Obande Obguinya ya ce an saba ka’ida wajen ayyana fitar da dan takarar gwamnan jam’iyyar ANDP a zaben na ranar 16 ga Nuwamban, 2019.
- Jam’iyyu 10 sun shirya taron dangi a zaben Ondo
- Sana’o’i: Gwamnati ta fara rabon tallafin N30,000
- Za a bude makarantun Gwamnatin Tarayya 12 ga Oktoba
Kotun ta kuma yi watsi da korafin jam’iyyar ANDP kan zaben a matsyin makararre bisa hujjar cewa an shigar da shi ne bayan cikar wa’adin da kundin tsarin mulki ya kayyade.
Don haka ta ce tun farko kotun sauraron karar zaben ba ta da hurumin sauraron kokin saboda lokacin yin hakan ya riga ya wuce.
Hukuncin na zuwa ne bayan Gwamna Diri ya daukaka karar kalubalantar hukuncin Kotun Sauraron Korafin Zaben na soke zabensa.
Da farko kotun karbar koken zaben ta yanke hukuncin ne kan soke takatakar dan takarar mataimakin gwamnan ANDP da INEC ta soke saboda bai kai shekara 35 da doka ta shardanta ba.