✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Gwamnan ya ce tsantsar ƙaunar da yake yi wa Tinubu ce ta sa ya sauya sheƙar zuwa APC.

Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne a hukumance a ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo, babban birnin jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan wasu kwanaki da ya shafe yana nuna sha’awarsa na sauya sheƙa.

A wani taron jama’a da aka gudanar a Ikot Abasi, ya ce: “Lokaci ya yi da za mu motsa” domin a haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta.

Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan shafe watanni uku yana tattaunawa da manyan mutane da masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya nuna godiyarsa ga PDP saboda goyon bayan da suka ba shi, amma yanzu lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiya gaba.

Ya bayyana cewa yana matuƙar ƙaunar Shugaba Bola Tinubu, kuma yana ganin Jihar Akwa Ibom za ta fi amfana idan tana aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya.

Gwamna Eno, ya sha alwashin cewa zai ci gaba da yi wa mutanen jihar aiki tuƙuru, ko daga wacce jam’iyya yake.

“Na kammala ganawa da jama’a a matsayin wanda kuka zaɓa, kuma na yanke shawarar komawa jam’iyyar APC,” in ji shi.

Gwamnonin jam’iyyar APC ne suka tarbe shi, ciki har da Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma; Bassey Otu na Jihar Kuros Riba; Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas; da Dapo Abiodun na Jihar Ogun.

Sauran da suka halarta sun haɗa da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta, Monday Okpebholo na Edo, da Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi.