✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Adamawa: Kotu ta tabbatar da takarar Binani

Kotu ta umarci INEC ta sanya sunan Sanata Binani a jerin ’yan takarar gwamnan Jihar Adamawa a zaben 2023.

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin ’yar takarar gwamnan Jihar Adamawa ta Jami’iyyar APC.

Kotun da ke zamanta a Yola ta jingine hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaben dan takarar gwamnan Jam’iyyar APC da Binani ta lashe.

Ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya sunan Sanata Binani a jerin ’yan takarar gwamnan Jihar Adamawa a zaben 2023.