Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma.
- Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha
- Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka
“Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna.
Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin hakan na haifar da rikici maras amfani.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ke bincike kan lamarin, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar kare hanyoyin kiwo da tabbatar da adalci wajen amfani da filaye.