Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya dakatar da alkalai 30 daga aiki bayan sun yi zanga-zangar rashin biyan su albashinsu na shekara biyu.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne ta bakin mukaddashin Babban Alkalin Jihar Kuro Riba, Eyo Effiom Ita kamar yadda Babban Magatakardan Jihar Edem N. Okokon, ya sanar.
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
- An kama limami da kan mutum
- Bom ya kashe sojoji 5, ya jikkata 15 a Borno
Sanrwar ta ce tun da gwamnatin jihar ta kasa biyan su tun bayan samansu alkalan kotun majistare a watan Fabarirun 2019, an dakatar da su daga zaman kotu hai sai abin da hali ya yi.
Mukaddashin Babban Alkalin Jihar wanda wa’adinsa ke karewa a mako mai zuwa ya umarci alkalan da aka dakatar da su ci gaba da zama a gida, inda zargi yawancinsu na da karbar rashawa domin su samu abin kashewa.
A makon da ya gabata ne alkalan kotunan majistaren suka yi zanga-zangar kwana uku a tsohon ofishin gwamnan jihar saboda rashin biyan su albashin shekara biyu.
Binciken Aminiya ya gano cewa bayan Gwamnatin Jihar ta sanar da daukar masu neman zama alkalan kotun majistare ne mutanen suka nema suka kuma yi nasara har gwamnatin ta tura su aka yi musu horo daga aljihunta.
Sai dai daga baya an ambato Gwamna Ayade na cewa ba da yawunsa aka dauke su aiki ba, ya kuma ki sanya hannu a daukar aikin nasu.
Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), reshen Jihar Kuros Riba, Paul Ebiala, ya shaida wa wakilin Aminiya a garin Kalaba cewa hukunce-hukunce sama da 1,000 da alkalan suka yanke za su tashi a tutar babu ke nan tun da ba su da halarci.