kungiyar dalibai ta kasa ta yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal saboda amincewar da ya yi a biya Naira miliyan 900 ga dalibai ’yan asalin jihar da suke karatu a makarantun ciki da wajen kasar nan. Kudin sun hada da kudin makaranta da alawus dinsu.
Shugaban kungiyar ta kasa, Kwamared Basheer Gorau ne ya yi yabon a wata sanarwar da ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a ranar Talata a Abuja.
“Muna yaba wa Mai girma Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal saboda ware Naira miliyan 900 domin biyan dalibai ’yan asalin jihar a Najeriya da sauran kasashen duniya, kudin makaranta ne da alawus,” inji shi. Ya ce Gwamnan ya cika alkawarin da ya yi wa daliban a lokacin da ya yi buda baki da su a karshen watan Ramadan.
Ya kara da cewa Jihar Sakkwato ce kan gaba wajen kula da walwalar dalibai a kasar nan, inda ya ce jihar ta kashe fiye da Naira biliyan uku da digo shida wajen bayar da tallafi ga daliban jihar.
Shugaban wanda ya yaba wa kokarin da Gwamnan ke yi wajen kyautata wa dalibai ya yi kira gare shi ya ci gaba da bullo da tsare-tsaren da za su inganta ilimi a jihar.