Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya fitar da jerin Sunayen mutum 17 da yake son nadawa kwamishinoni a Jihar.
Sakataren gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya fitar da sunayen da gwamnan zai aike wa majalisa domin tantancewa.
- Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta soke lasisin Kannywood
- Abdourahmane Tchiani: Wane ne shugaban gwamnatin sojin kasar Nijar?
Sunayen su sun hada da Laftanar Kanar Abdullahi Bello da Sanusi Ahmed Maidala da Abdulkadir Mohammed Waziri da Adamu Inuwa Pantami da kuma Mohammed Saidu Fawu.
Sai kuma Mijinyawa Ardo Tilde da Mohammed Shetima Gadam da da Babban Sakataren hukumar tattara kudaden shiga na jihar Salihu Baba Alkali.
Sauran su ne Babban Daraktan BESDA Dokta Abdullahi Bappah Garkuwa da kuma tsohuwar ’yar majalisar dokokin jihar mai wakiktar Shongom, Asma’u iIganus.
Sai kuma tsohuwar kwamishinar Ilimi Dokta Aishatu Umar Maigari da tsohon kwamshinan kudin jihar, Mohammed Gambo Magaji da tsohon kwamishinan shari’a Barista Zubairu Umar da tsohon Kwamishinan Lafiya Dokta Habu Dahiru.
Har ila yau akwai Tsohon Kwamishinan Kasuwanci Alhaji Nasiru Gwani da Barrnabas Malle da Maijama’a kallamu da sannan sai